HAUSA NEWS

Gamnatin Kano ta yi gargadin daukar tsatstsauran mataki ga masu karkatar da kayan abinci

Jigawa Post

Gwamnatin jihar Kano ta ce zata ɗau tsatstsauran mataki ga duk wanda ta kama da karkatar da kayan abincin da gwamnati ta bayar a rabawa al’umma domin rage musu raɗaɗin matsin rayuwa da ake ciki a wannan lokaci.

Gwamnan jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan yayin da yake ƙaddamar da bayar da tallafin kayan abinci karo na hudu a yau ga al’ummar jihar na ƙananan hukumomi 44.

Karin Labarai:Gwamnatin Jigawa Ta Bada Tallafin Littattafan Ilmantar Da Alhazai Aikin Hajji

Da yake ƙaddamar da kayan gwamna Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da cewa wa’innan kayan abincin za’a raba su ne ga dukkanin mazaɓu 484 da suke faɗin jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa gwamna Abba Kabir Yusuf yayi kira ga dukkannin wa’inda aka dorawa alhakin raba kayan da su kasance masu tabbatar da gaskiya da adalci.

About the author

admin

Add Comment

Click here to post a comment