HAUSA NEWS

Mun haramta yin Films din dake nuna fadan daba da harkar daudu a jihad Kano- El-mustapha.

Jigawa Post

Biyo bayan korafe-korafen da al’umma keyi a kan shirya fina-finan dake nuna fadan Daba da harkar Daudu a jahar Kano. Shugaban Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta jahar Kano Abba El-mustapha ya bada umarnin dakatarwa tare da hana dukkan fina-finan dake nuna fadan Daba da harkar Daudu a fadin jahar Kano.

Abba El-mustapha na  bada wannan umarni ne a ranar laraba 3 ga watan Aprilu, 2024, jim kadan bayan wata ganawa da yayi da manyan ma’aikatan  Hukumar tace fina-finan na Kano tare da wasu daga cikin wakilan yan masana’antar shirya fina-finan ta kannywood wanda suka hada da kungiyoyin MOPPAN, AREWA FILMS MAKERS, DIRECTORS da kuma PRODUCERS.

Abba ya kara da cewa doka ce ta bawa Hukumar damar dakatarwa ko hana duk wani film da take ganin yaci karo da tarbiya tare da al’adar  al’ummar dake jahar, a saboda haka tuni lokaci ya shige da za’a saka ido irin wannan gurbatattun fina-finai su cigaba da yaduwa a cikin al’umma.

Abba El-mustapha ya godewa yan masana’antar shirya fina-finan ta kannywood dangane da hadin Kai da kuma goyan bayan da suke bawa Hukumar a koda yaushe.

A ya godewa al’ummar jahar Kano kan irin hadin kan da suke bawa Hukumar musamman na sanar da ita duk wani abu da suke ganin ya saba da al’ada tare da tarbiyar addinin musulunci.

Abba El-mustapha ya kuma yi alkawarin cigaba da barin kofar sa a bude domin karbar shawarwari ga duk Wanda suke da bukatar hakan.

Akarshe ya bawa masu shirya irin Wannan fina-finan damar wata daya dasu gyara aiyukan nasu kafin dokar ta fara aiki gadan-gadan a kan su.

About the author

admin

Add Comment

Click here to post a comment