WASANNI

Man United na son maye gurbin Ten Hag da Motta, Arsenal na son FayeThiago Motta

By Jigawa Post

Sa’o’i 6 da suka wuce
Manchester United na son nada kociyan Bologna Thiago Motta domin maye gurbin Ten Hag. (Gazzetta dello Sport)

Amma kuma hukumar zartarwar kungiyar ta Manchester United za ta jira har zuwa karshen kakar da ake ciki ta yanke shawara a kan Erik ten Hag, duk da matsin lambar da ake yi wa kociyan. (Times)

Arsenal ta bi sahun kungiyoyi irin su Manchester United da Bayern Munich wajen duba wasan matashin dan bayan karamar tawagar Barcelona, Mikayil Faye kafin zawarcinsa dan Senegal din mai shekara 19, a bazara. (Mail)

Dan wasan tsakiya na Manchester City Kalvin Phillips, na Ingila wanda yanzu yake zaman aro a West Ham, ya zama cikin jerin wadanda Fulham ke son saye a bazara. (Football Transfers)

Read Also:Gwamnatin Jigawa Ta Bada Tallafin Littattafan Ilmantar Da Alhazai Aikin Hajji

Ribado, Badaru, Matawalle da dakarun mu sun chanchanci yabo da addu’a-Ilallah

Amma kuma Phillips zai iya sake komawa kungiyar garinsu, Leeds United idan har za ta biya abin da ya kama daga fam miliyan 30 zuwa 40. (Football Insider)

Manchester City na son saka wa Rodri ta hanyar kara wa dan wasan na tsakiya na Sifaniya albashin da zai sa ya ci gaba da zama a kungiyar har karshen sana’arsa ta kwallon kafa. (Mirror)

Arsenal da Chelsea na son Viktor Gyokeres amma kuma Sporting Lisbon ba za ta karbi abin da yake kasa da yuro miliyan 100 ba a kan mai kai harin dan Swede.

Atletico Madrid na sha’awar dan wasan tsakiya na Fulham Andreas Pereira, na Brazil mai shekara 28.

Kwatsam an bayyana tsohon kociyan Chelsea da Everton Frank Lampard a matsayin wanda za a ba aikin horda da tawagar Kanada.

Aaron Ramsdale zai bar Arsenal a bazaran nan, kuma ana sa ran zai tafi Newcastle United ne.

Liverpool na tattaunawa da Trent Alexander-Arnold a kan sabon kwantiragi.

Dinamo Zagreb ta biya wata talla ta cikakken shafi a babbar jaridar wasanni ta Sifaniya, Marca, domin shawo kan dan wasan tsakiya na Croatia Luka Modric, mai shekara 38, ya koma kungiyar wadda ita ce kungiyarsa ta farko, idan har zai bar Real Madrid a bazaran nan.

Paris St-Germain ta dakatar da tattaunawar sabunta kwantiragi da kanin Kylian Mbappe, Ethan Mbappe, mai shekara 17, kuma kwantiragin matashin na tawagar Faransa ta ‘yan kasa da shekara 16, zai kare ne a watan Yuni.

Sevilla za ta sayar da dan wasan da ya fi ci mata kwallo Youssef En-Nesyri, kuma kungiyoyin Premier na harin dan Morokon mai shekara 26.
(BBC)

About the author

admin

Add Comment

Click here to post a comment