HAUSA NEWS

Ribado, Badaru, Matawalle da dakarun mu sun chanchanci yabo da addu’a-Ilallah

By Ahmed Ilallah

Kamar yadda kowa ya sani ne, babu mummunan abun da ya ke  damun Talakan Nigeria, musamman na Jahar Zamfara, Katsina, Kaduna, Niger, Sokoto da sauran, kamar rashin tsaro da yawaitar Yan Ta’adda.

Tsananin rashin tsaro ya haifar da masifu kala-kala, ya karawa alummar wannan wurare talauchi, ya hanasu Noma da ma dukkanin sana’oi, ya mai da dewa yan gudun hijira, karbar kudin fansa ya talauta su.

Tabbas, nasarorin da dakarun tsaron kasar nana suka samu da kashe dubban Yan bindigar daji da Yan Ta’addar da suka jima suna cin karen su babu babbaka a wannan jahohi, ba karamar nasara bace.

Kamar yadda ruhotanni  suka bayyana nasarar hukomin tsaron wannan kasa a wannan watanni uku na kashe manya manyan shugabannin Yan Ta’adda  guda goma da kuma hallaka Yan Ta’adda 2,351, da kuma kama wasu 2,308 da ceto mutanen da a kayi garkuwa dasu kimanin 1,241, ba karamar nasara bace a wannan yakin da Yan Ta’adda suke addabar al’ummah.

Tabbas, dukkanin jami’an tsaran mu sun chanchanci a yaba musu a kuma kara taya su da adu’ar Allah ya kara musu nasara, ya kara kare su a cikin aiyukan su.

Kara karantawa:Gwamnatin Jigawa Ta Bada Tallafin Littattafan Ilmantar Da Alhazai Aikin Hajji

Mun haramta yin Films din dake nuna fadan daba da harkar daudu a jihad Kano- El-mustapha.

Nuhu Ribadu, Babban mai bada shawarar tsaro na kasa, da Babban Ministan Tsaro Badaru Abubakar da Karamin Ministan Tsaro Matawalle, da ma sauran jagororin tsaron wannan kasa, wanda bisa jagorancin su a ka sami wannan nasara.

Akasarin masu sharhi da bibiyar rashin tsaro a wannan kasa, sunyi imanin cewa an soma samun galabar wannan yakin.

Kashe wadannan shugabannin Yan Ta’adda da mambobin su, ba karamin tasiri zai yi ba wajen kawo karahen Ta’addanci a wannan jahohi.

Tabbas matsalar rashin tsaro na kowa da kowa ce, kowa zai iya bada gudun mawar sa, koda ta hanyar addu’ace.

About the author

admin

Add Comment

Click here to post a comment