News

‘yanmata 4 sun mutu a cikin tafki a Jigawa

Daga Ali R. A, Dutse

Akalla ‘yan mata 5 ne suka nutse a ruwa a tafkin Malkaderi da ke karamar hukumar Gagarawa ta jihar Jigawa a ranar Asabar 28 ga Satumba, 2024. 

DSP Lawan Shiisu Adam, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar ne ya sanar da haka ga manema labarai a Dutse a ranar Lahadi 29 ga Satumba, 2024.

Shi’isu ya ce wadan da suka su ka rasa rayukan na su sun hada da Saina’u Musa, 12, Fiddausi Ado, 11, Habiba Musa, 12, and Bahijja Musa, 13, yayin da aka ceto rayuwar Sahura Auda mai shekara 8 cikamakon ta 5 din.

Lawan ya ce rundunar ‘yan sandan jihar ta yi gaggawar kaddamar da aikin cetoa lokacin da aka fadamata faruwar lamarin tare da mutanen gari da su ka iya Iyo. 

Ya ce Jami’an na su sun kwashe wadanda lamarin ya rutsa da su daga tafkin, aka kai su cibiyar kiwon lafiya a matakin farko ta Gagarawa, inda aka tabbatar da mutuwar ‘yanmatan hudu.

Kwamishinan ‘yan sanda, CP AT Abdullahi, ya mika ta’aziyya ga iyalan mamacin tare da yi musu addu’ar Allah ya bawa wacce ta rayu lafiya.

About the author

admin

Add Comment

Click here to post a comment