Labaran Hausa

Gwamnatin Jigawa Ta Bawa Matasa 300 Jari da runfunan shaguna na zamani

Daga Ali Ali Rabiu, Dutse

Asabar, 21 ga December, 2024

A wani gagarumin yunkuri na shawo kan matsalar rashin aikin yi da samar da ci gaban tattalin arzikin matasa, Gwamnan Jihar Jigawa Umar Namadi ya kaddamar da wani shirin inganta rayuwar jama’a, inda ya raba kantunan ga matasa 300 a karkashin wani shiri mai suna ‘Micro Retailers Empowerment Initiative’ na jihar. 

Shirin da ke da nufin rage sauye-sauye da kuma kara samar da ayyukan yi a tsakanin matasa, wani bangare ne na kokarin da gwamnatin jihar ke yi na daukaka al’ummarta.  

Matasan da suka anfana da shirin

Wadanda suka ci gajiyar shirin, wadanda aka zabo ne a tsanake daga mazabu 287 da ke fadin jihar, an basu kayan aiki da horar da su don kaddamar da harkokinsu. 

Wannan shiri wanda hukumar samar da ayyukan yi da wayar da kan matasa a karkashin jagorancin Habibi Ubale ke kula da shi, ya kara jaddada kudirin gwamnatin na karfafawa matasa gwiwa da tallafa wa kananan ‘yan kasuwa. 

Karin Labari:GBV: Kawo Karshen Cin Zarafin Mata Na samun Cigaba A Jigawa.

Da yake jawabi a wajen kaddamar da shirin, Gwamna Namadi ya jaddada cewa shirin ya yi daidai da ajandar kawo sauyi na shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu domin karfafa matasa da bunkasa harkokin tattalin arziki a fadin Najeriya. 

Ana sa ran wannan shirin zai inganta rayuwar matasa, zai kuma kara habaka tattalin arziki a fadin jihar Jigawa, tare da kafa ma’auni ga sauran jihohi don su yi koyi da shi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button