Daliban Jigawa Sun Lashe Gasar Tantance Kalmomi (Spelling Bee) A Abuja
Tawagar ta samu jagorancin Magaji Ibrahim, mataimakin darakta a ma’aikatar ilimi matakin farko ta jihar jigawa
Daga Ali Ali Rabiu
Tue, 24th Dec, 2024
A wani gagarumin baje kolin nagartaccen ilimi, dalibai daga jihar Jigawa sun yi nasarar samun lashe gasar tantance kalmomi (Spelling Bee) da aka gudanar a tsakanin jihohin kasar nan da aka gudanar a Abuja ranar 20 ga watan Disamba, 2024.
Wannan nasarar da aka samu wata shaida ce ta jajircewar jihar wajen ganin ta samar da ingantaccen ilimi, wanda gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi da ma’aikatar ilimi ta kasa ke marawa baya.
Tawagar da ta lashe gasar ta kunshi dalibai uku da suka hada da Almustapha Inuwa Dutse daga makarantar Dutse Capital, Shidaya Sani daga Model Boarding Primary School (MBPS) Gumel, da Fevour Onnen daga makarantar Dutse Capital.
Tawagar ta samu jagorancin Magaji Ibrahim, mataimakin darakta a ma’aikatar ilimi matakin farko ta jihar jigawa. In da ya yabawa daliban wajen nuna bajintar harshen turanci da sanin kalmomi.
Gasar dai ta samu halartar wasu makarantu biyar da ke babban birnin tarayya Abuja da kuma jihar Jigawa. Makasudin gudanar da gasar shi ne a kara kaimi da harshen Ingilishi a tsakanin dalibai.
Tawagar da ta yi nasara ta samu lambar yabo daga Mal Ahmad Abubakar, shugaban taron, Mal Abdulkudus Kubuwa, da Mal Mustapha Ahmad, mambobin kwamitin alkalai.
Daga nan sai Magaji Ibrahim ya ja hankalin daliban da su jajirce wajen ganin sun nuna kwazo da kuma wakilcin jihar a gasar kudan zuma ta nahiyar Afirka a shekarar 2025.
Wannan nasarar ta nuna kwazo da daliban ke yi a jihar Jigawa, wanda ya share fagen samun nasarori a nan gaba
One Comment