GBV: Kawo Karshen Cin Zarafin Mata Na samun Cigaba A Jigawa.
Daga Asmau Abdullahi, Dutse
Sun, 15th Dec, 2024
Kawo karshen cin zarafin Mata a Jigawa yana samun daukar kwararan matakai wajen Kawo karshen sa kama daga kudurai da Gwamnati ke dauka zuwa ga tsare tsaren cikin Al’umna da masu ruwa da tsaki na aiki tukuru domin samo sahihiyar hanya wajen tafiyar da al,umma bai daya.
Ma’aikatar mata da walwalar al’umma karkashin shugabancin kwamishiniyar mata ta Jigawa Hajiya Hadiza T. Abdul Wahab na yin kokari matuka wajen yaki da wannan ta’ada.
Hukumar kididdiga da tantance karuwar yawan A’lumma da lafiyar su a nigeria wato( NDHS ) 2018 tace daya daga cikin Mata uku sun fuskanci nauin cin zarafi kama daga duka fyde da sauransu.
Wannan gididdigar ta jawo hankalin Gwamnati wajen daukar matakan gaggawa domin kare hakki da martabar Mata. Wannan matsala tana da nasaba da yanayin rauni na Mata akan Maza a cikin al’umna, da rashin karfin na damar mallakar tattalin arziki da fada aji wajen gudanar da rayuwa a cikin al’umna.
wannan banbancin yasa ake daukar mata tamkar basuda daraja yasa suke fuskantar tsangwama,cin zarafi da wulakanci .
Tunani irin na gargajiya da A’lada a lokutan baya suna kallon Mata a cikin al’umna tamkar marasa daraja da kima ta Dan Adam Wadannan Al’adun gargajiya sun haifar tare da wanzuwar cin zarafi da wulakanta Mata ta kirkirar wasu dabaru na nuna rashin darajar su da maida su masanaantar haihuwa da rainon yara a cikin al’umna.
Dogaro da yawancin Mata keyi da mazajen su na tattalin arziki watakila saboda rashin ilmin da samun damar aiki mai nagarta daidai da wanda Maza kanyi. Wannan yanayin kan iya jefa mata cikin mawuyacin hali.
Rashin gata da kariya ko zartar da Doka ya kara taazzara cin zarafin matan , Koda Dokar tana aiki tsoro da jin kunya, rashin goyon baya da tabbas wajen zartar da sharia ta gaskiya babbar barazana ce.
Wata Al’umnar ta dauki kaskanta Mata a matsayin nau’in gyara da ladabtarwa, Mata maza harma da wasu manyan sun yarda cewa cin zarafi ko take hakkin mata wata halartacciyar hanya ce ta neman shugabanci ko sasonta rigima.
Wannan wayewar a ciki wasu A’lumma kan Kawo nakasu ga Aiwatar da Dokar cin zarafin Mata wata Gender base violence. (GBV) Dimuwa da firgita ga matan da aka ci zarafi kan iya shafar kwakwalwarsu su samu tabin hankali ya zama wahala wajen fita daga cikin wannan hali.
Rashin ilmi da wayarda Kai a wasu A’lumma kan hakkokin Mata da gudunmawarsu yana Kawo karuwar cin zarafin matan, Maza da Matan basu fahimci illar wannan dabia ba saboda tarbiyar Gargajiya da A’lada.
A bisa wadannan daliliai ne Gwamnati ta fito da Dokar nan wato (VAPP) Dokar hana cin zarafin Dan Adam 2015 Wanda ta kunshi duk wani cin zarafin Dan Adam, Wannan Doka ta samu karbuwa a duk jihohi 36 na kasar Nan. A shekara ta 2018 kididdiga ta nuna duk daya daga cikin Mata uku sun fuskanci nauin cin zarafi a nigeria kama daga fyde, duka da nuna wariyar jinsi, Karuwar wannan matsalar ya nuna bukatar daukar matakan gaggawa domin kare yanci da hakkokin Mata.
Gwamnati ta kafa hukumar hana fasa gwauri da fataucin mutane wajen hada karfi guri daya da masu ruwa da tsaki domin dakilewa da hana cin zarafin Mata, Hukumar ta samar da wata kafa da ke kai korafi nan take na cin zarafin matan da zarar ta samu rahoto tare da basu tallafi domin kyautata rayuwarsu.
Jihar jigawa tana daya daga sahun gaba na Kawo karshen cin zarafin Mata a yayinda ta samar da Maikatar da ta shafi hakkokin Mata wato Women Affairs da ke kula da tsare tsare na Mata da Yara.
Gwamnati jigawa ta rattaba hannu a Dokar da ta tanadi kisa ga duk wanda ya aikata fyde Kuma yana dauke da cutar Mai karya garkuwar jiki wato HIV virus. Ipas Nigeria da hadin gwiwar shugabannin majalisar jihar jigawa sun gudanar da ayyukan fadakarwa tare da masu ruwa da tsaki domin ciyarda Dokar VAPP Act gaba wajen daukar nauyin shiri na musamman a gidajen Radio dake fadin jihar ganin tabbatar da nasarar Shirin.
Gwamnatin jihar ta kara samar da wani tsari Mai suna State Gender management system (SGMS) wato wani tsari da sake duba fasalin dangantaka tsakanin jinsi da irin gudunmawar da suke badawa a cikin al’umna. A shekara ta 2021 karkashin Gwamnatin Muhd Badaru Abubakar ta sanya hannu akan Dokar kula da kariya ga kananan Yara.
Kungiyoyin Farar hula suna taka mahimmuyar rawa wajen dakilewa da kawo karshen Matsalar, Sarakunan Gargajiya da shugabannin addini suna taka rawa wajen daukar nauyin wayarwa da kira ga jamaa su kula da hakki da martaba a kowane yanayi na rayuwarsu.
Masu martaba Sarakunan Masarautun jihar jigawa, Hadejia, Gumel, Kazaure,Dutse da Ringim na taka gagarimar rawa wajen kawo karshen cin zarafin Mata a jigawa.
Gwamnati da Kungiyoyin fafutikar kare hakkin Mata da saura al’umma na da bukatar hada Kai ayi aiki tare domin samar da kariya da Girmama Mata, Manyan Malaman addini suna gagarimin aiki wajen kauda banbancin darika tsakanin su domin samun nasarar Shirin.
Akwai bukatar Gwamnati ta kara kudin gudanar da Shirin domin samun sakamako mai kyau. Karawa Dokar karfi da zata kunshi duk wani cin zarafin Dan Adam kama daga cin zarafia cikin gida, fyade da lalata tattalin arzikin cikin sani na Dan Adam, karfafa Dokar da zata hana auren wuri na kananan yara Mata , kaciyar Mata da cin mutuncin wasu iyalin domin daga darajar wasu.
Karfafawa da gudanar da taro domin wayarda da Kai na sabanin fahimta da wasu ke yiwa Dokar ko Shirin kare cin zarafin Mata saboda gurguwar fahimta addini da rashin ilmi. Wayarwa da Maza da Mata Kai su fahimci mahimmancin Girmamawa da kaunar juna.
Akwai bukatar Gwamnati da masu hannu da shuni su cigaba da daukar nauyin Mata kama daga karkara zuwa birane wajen basu da koyamusu sanaoi na dogaro da Kai domin tsayawa da kafarsu. Bukatar bada goyen bayan Mata su shiga a dama dasu a gudanar da shugabanci a cikin al’umma daga kasa har sama.
Gwamnati ta samarwa da Mata ingantattun hanyoyin lafiya da kayan aiki a dakunan haihuwa da inganta shayarda jarirai domin su fita daga tsangwama da illolinta. Akwai bukatar a samar wa Mata hanyoyi na sirri wajen kaiwa rahoto cikin sirri a duk lokacin da bukatar haka ta taso tare da bada kariya ta musamman.
Akwai bukatar Gwamnati ta samar kwararrun jamiai masu kula da matan da suka sami tabin hankali ta dalilin cin zarafi ko fyade da bawa jamian koyarwa ta musamman wajen gudanar da Shirin.
Dole ne a samarda wani shiri na zakulo Maza da Mata da basu horo gudanarda Shirin hana cin zarafin a karkara da birane da Matakin tarayya da na jihohi. Fitowa da Shiri wanda zai kalubalanci dab’u da al’adu na cin zarafi da kara karfafa wanzuwar yanci da mutumcin Mata .
Akwai bukatar bawa jamian tsaro da masu sharia horo na musamman yanda zasu gudanar da sharia ta cin zarafi ba tare da nuna banbanci ko son kai ba.
Gwamnati ta samar da kafar gudanar da binciken ko ta kwana da tabbatar da hukunta masu laifin. Akwai bukatar amfani da wata hanya ta tattara bayanai domin sanarda hukuma a guraren da Matsalar tafi kamari domin samun Karin kudin gudanarwa.
Gayyatar Kungiyoyin kasashen ketare da hadin gwiwar na cikin gida zaiyi tasiri wajen Kawo karshen Matsalar. Bada goyon baya da yarjejeniya da aka cimma kamar kudurin majalisar dinkin duniya {SDGs ) da hukumar kauda duk wani nau’in nuna banbanci akan Mata wato ( CEDAW ) Wanda ke rajin Kira da kauda cin zarafin Mata. Wannan zai taimaka wajen kauda Matsalar cin zarafin Mata a Jigawa.
A garin hadejia dake jihar jigawan munci karo da yarinya yar shekara 10 da wani Dattijo dan shekara 60 yayiwa fyde ta dauki ciki ya kuma tsere, a hira da mukayi da mahaifiyar Amina tace(‘ Wannan Yarinya marainiya ce amma munyiwa Allah godiya kungiyar mata da shugaban karamar hukumar hadejia sun dauki nauyin kula da Amina har ta haihu sun kuma bamu tallafin kudi da abinci da alkawarin karatun ta.’).
Nayi hira da wata mai tabin hankali da wani da baa sani ba yayi mata ciki inda wata kula da ita ta shaida min cewa (‘ Nike kula da ita amma yanzu karamar hukumar hadejia da kungiyar mata ta Woman foundation sun dauki nauyin kula da lafiyar ta da jaririn da ta haifa.’).
Wani Mahaifi yayiwa yar’sa ta cikinsa ciki a garin Dutse,Yarinyar Mai shekara 16 ta shaidamin cewa (‘ Ni banta sanin wani Da namiji ba idan banda Mahaifina ‘) A halin yanzu yana hannun hukumar Yan sanda ana bincike kafin a mekashi kotu ya girbi abinda ya shuka .
2 Comments