Labaran Hausa

Bayan Tabbatar da DUTSE GREAT WATER PROJECT; Saura HADEJIA IRRIGATION PROJECT PHASE II

...Wannan aikin yana da muhimmanci a wannan lokacin,
Ahmed Ilallah Tue, 24th Dec, 2024

Tabbas Maigirma Gwamna yayi namijin kokari na kaddamar da wannan gagarumin aiki da Gwamnonin baya suka sha fama a kan wannan aikin, har ma wasu Gwamnonin suka sami sabani da shugabannin su a kan wannan aiyukan.

In zamu iya tunawa a shekara ta 2013 an samu danbarwa a Jama’iyya mai mulki ta PDP da wasu Gwamnoni guda bakwai, wanda suka tsagi Jama’iyar PDP don yunkurin kafa nPDP, a chikin wannan Gwamnonin har da na Jigawa, wato Sule Lamido.

Read Also:Addressing NNPCL’s Misinformation-Dangote

Bayan chikumurda da a kayi a wannan lokacin, Sule Lamido yayi magana a wata hira da yayi a gidan redion BBC, daga dalilan sa na wannan bore akwai kin aiyuka guda uku muhimmai da Gwamnatin Tarayya taki yi a Jigawa, wanda suka hada da Dutse Great Water Project, Hadejia Irrigation Project da kuma Titi daga Kwanar Gamayin-Kafin Hausa-Jahun-Ajingi.

A halin yanzu, tun a shekarar 2017 Gwamnatin Shugaba Buhari ta bayar da kwangilar yin wannan hanyar, sai gashi a yanzu wannan Gwamnatin ta kaddamar da aikin Ruwan Dutse da kewaye, Alhamdulillah.

To a yanzu ma, Maigirma Gwamna ya Kamata a sake rokar Shugaban Kasa Tinubu a kan kammala wannan aikin da ya kai tsawan shekaru arba’in.

Wannan aikin yana da muhimmanci a wannan lokacin, zai taimaka wajen cika burin gwamanatin Jahar Jigawa na bunkasa noma da korar yunwa. Zai samawa dubban mutane aiyukan yi, zai rage yawan kudaden da manoma suke kashewa, wajen fetur da injinan bayi.

Zai taimakawa Shugaba Tinubu na cimma burin sa, na Renewed Hope Agenda, musamman wajen samar da aikin yi da samar da abinci.

A gwamnatin baya an yi yunkurin yin wannan aiki, amma ba a kai ga yi ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button