Labaran Hausa

Ma’aikatan Jigawa na murna da gwamnati ta fara biyan sabon albashi

…inda suka bayyana farin cikin su da fatan alkhairi ga Gwamnan jihar Malam Umar Namadi. 

Daga Ali Ali Rabiu, Dutse

Talata 24 ga December, 2024

Gwamnatin jihar Jigawa ta fara biyan sabon mafi karancin albashi na N70,000.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar Jigawa Alhaji Muhammad K Dagaceri.

Ya ce tuni wasu ma’aikata suka samu sanarwar banki na albashin watan Disamba.

Ya yi kira ga ma’aikata a Jihar da su mayar da martani ta hanyar sadaukar da kansu ga aiki tare da marawa Gwamnati baya domin ci gaba da gudanar da kyakkyawar alakar aiki.

Karin Labari:Daliban Jigawa Sun Lashe Gasar Tantance Kalmomi (Spelling Bee) A Abuja

Idan za a iya tunawa, Gwamna Malam Umar A Namadi ya sanar da amincewa da biyan sabon mafi karancin albashi daga ranar 1 ga Disamba, 2024.

Jaridar Jigawa Post ta zanta sa wasu ma’aikatan jihar da suka fara sabon nasu inda suka bayyana farin cikin su da fatan alkhairi ga Gwamnan jihar Malam Umar Namadi. 

Sun bayyana cewa suna ganin hakan almarace da ba za fara biyan su albashin ba daga wannan wata sai suka ga abin ba haka bane. 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button