HAUSA NEWS

Gwamnatin Jigawa Ta Bada Tallafin Littattafan Ilmantar Da Alhazai Aikin Hajji

Daga Edita

Gwamnatin Jihar Jigawa ta baiwa hukumar jin dadin Alhazai ta jihar da kuma hukumar kula da ilimin addinin musulunci gudunmawar kwafin litattafai dubu biyar mai suna “GUZURIN MAHAJJATA” da nufin karfafawa maniyyata ilimi da shirye-shiryen tafiya kasa mai tsarki.

Da yake mika littattafan ga shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai da Babban Sakatare na Hukumar Ilimi ta Musulunci, Alhaji Ahmed Umar Labbo da Dokta Mubarak Abdulwahab Hassan, Sakataren Gwamnatin Jiha, Malam Bala Ibrahim ya ce wannan karimcin na daga cikin kudirin gwamnatin jihar na don sauƙaƙa tafiya da gudanar da aikin Hajjin cikin sauki ga Mahajjatan jihar.

Malam Bala Ibrahim ya jaddada kudirin gwamnatin jihar na samar da dukkanin abubuwan da suka dace ga maniyyatan.

Read Also:JIGAWA: Council Chairman Berates Boarder Community Development Agency For Poor Performance-Jigawa Post

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta yanke shawarar daukar nauyin buga kwafin litattafai guda 5,000 domin karfafawa maniyyata ilimi da kuma shirye-shiryen tafiyarsu kasa mai tsarki.

A jawabinsa, shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya gode wa gwamnati bisa wannan karimcin.

Shugaban, wanda Daraktan Yada Labarai na Hukumar Malam Murtala Abdu Babura ya wakilta, ya yaba wa Gwamna Umar Namadi bisa bayar da tallafin Naira miliyan daya ga Alhazan jihar.

A lokacin da yake bitar littafin, Malam Mahmud Yunusa ya bayyana cewa littafin yana da matukar muhimmanci ga Jagorar aikin hajji, inda ya ce yana da kyau Alhazan su karanta shi, da ma masu son koyon Fiqhu da ladubban aikin Hajji.

Malam Mahmud Yunusa ya yabawa marubucin littafin aikin, tare da godewa Gwamna Umar Namadi bisa jajircewarsa na ci gaba da kyautata jin dadin alhazai a kowane lokaci.

Radio Nigeria Kaduna

About the author

admin

Add Comment

Click here to post a comment