Labarai

Gwamnatin Jigawa ta dage dokar hana fita baki daya

Jigawa Post. wallafawa ranar Talata13 Agusta, 2024

Gwamnatin jihar Jigawa ta janye dokar hana zirga-zirga a kananan hukumomin jihar gaba daya.

Kwamishinan yada labaran jihar Alhaji Sagiru Musa Ahmad ne ya bayyana haka a gidan gwamnatin jihar Jigawa Dutse jim kadan bayan kammala zaman majalisar tsaron jihar ranar litinin 12 ga watan Agustan 2024, karkashin jagorancin gwamna malam Umar Namadi.

Kazalika kwamishinan ya kara da cewa gwamnan jihar malam Umar Namadi ya kuma yiwa alummar jihar godiya kan hakuri da addu’a in da suka taya gwamnatinsa har wannan kura ta lafa.

About the author

admin

Add Comment

Click here to post a comment