HAUSA NEWS

Kamfanin ATRI Hadin gwiwa da AGROCORP sun horar da manoma 5,000 a Jigawa

Jigawa Post: Sun, 18th Aug, 2024

A wani bangare na inganta walwala da zamantakewar jama’a, Kamfanin hada-hadar noma na ATRI Commodities Nigeria Ltd hadin gwiwa da AGROCORP ya horar da manoma kimanin 5,000 kan kyawawan manufofin inganta Ayyukan Noma (GAP).

Rahotanni sun ce kamfanin ya bullo da dabarun ne domin jaddada amfani da takin gargajiya maimaikon amfani da na zamani wanda akasari ake samu daga takin dabbobi da tarkacen bola.

Read Also:Gwamnatin Jigawa ta dage dokar hana fita baki daya

Manajan reshen kamfanin, Mista Rahul Chodankar ya bayyana haka yayin kaddamar da shirin kashi na farko da aka gudanar a garin Yandutse da ke karamar hukumar Ringim.

Chidankar ya ce an yi shirin ne da nufin ilmantar da manoma domin ceto manoma da suke kashe makudan kudade wajen siyan taki (NPK da Urea) a maimakon haka sai su yi amfani da takin gargajiya.

Mista Rahul ya jaddada cewa, kamfanin ya horar da manoman kyauta domin inganta noman su maimakon sayo takin kan farashi mai tsada, inda ya tabbatar dacewa suna fatan tsawaita ayyukan bada dabarun horon manoman ya kai 10,000 a shekara mai zuwa.

Ya ce:- “Mun bai wa manoma 5,000 horon ne kyauta ba wanda ya bada ko da sisin 5,000 a fadin Jihar Jigawa tare da jawo karin manoma a matsayin wadanda za su ci gajiyar aikin a kakar noma ta badi kuma mun gudanar da irin wannan shiri ne a wasu Jihohin Tarayya kamar Kwara, Nasarawa, Kano da Jigawa”.

Jaridar Hotpen ta ruwaito cewa, Kamfanin noma mai zaman kansa ATRI Commodities Nigeria Ltd mai taken ‘Abokin Manoma’ ya horas da manoman ridi a kananan hukumomi 16 a jihar Jigawa da suka hadar da:- Kaugama, Maigatari, Birniwa, Guri, Ringim, Taura, Gagarawa, Garki, Suletankarkar , Gumel, Kafin Hausa, Auyo, Malam Madori, Jahun, Miga da Gwaram.

Da yake jawabi, Manajan CRS ATRI Commodities Nig. Ltd, Dzahemen S. IIiambee ya ce horon da aka yi wa manoman ridi zai taimaka musu wajen samun kudaden da za su samu.

“Manomi na da zabin sayan buhun NPK guda 1 kacal a kan Naira 40,000, akwai yiwuwar manomi ya yi aiki da buhu 3-4, kaga kudin da yawa kusan naira dubu 120,000 ko 160,000, idan kuwa ya yi amfani da takinsa na gida (Amalanke daya) akan Naira 1500 zuwa N2000 kacal, ma’ana zai iya amfani da guda 20, ba zai kashe kudin da ya wuce dubu 40 ba”.

Ya jaddada cewa fa’idar amfani da takin gida da manoma ke yi, zai iya daukar shekaru biyar ba tare da an sake zubawa gonar taki ba, amma kun ga amfani da NPK da Urea dole ne a duk lokacin aikin noma.

IIiambee ya yi kira ga manoman da su yi amfani da abin da suka koya yayin bada horon, kamfanin ya kuma horar da manoma yadda za a shawo kan zaizayar kasa.

Daya daga cikin mata manoman da suka ci gajiyar shirin, Hajara Ismail Yan-dutse ta bayyana godiya ga kamfanin ATRI bisa irin kwarin gwiwar da yake bai wa manoman ridi domin inganta noman su.

About the author

admin

Add Comment

Click here to post a comment