Jigawa Post Hausa

SAYEN JAMI’AR KHADIJA: Shin Wane Alfanu Zai Kawowa Jihar Jigawa?


Daga Ahmed Ilallah

A wannan makon ne, Majalissar Zartarwa ta Jahar Jigawa ta sanar da kammala sayen Jami’ar Khadija (Khadija University Majiya) a kan Naira Biliyan 11, daman tun a watannin baya Gwamnatin Jahar ta kafa wani Kwamati da zai duba yiyuwar sayen Jami’ar mai zaman kanta dake da ke karamar hukumar Taura.

Bayan da tabbatar da sayen wannan Jami’ar, da kuma bayanen da ra’ayi ma banbanta, a game da wannan cigaba.

Amma shin a kwai alfanu a sayen wannan Jami’a? Bisa la’akari da yanayin da ilimi yake a wannan lokaci a Jahar?

Shin a wane matsayi ilimin gaba da sakandare yake a Jigawa?

Jahar Jigawa da take da yawan al’ummar da suka kai kimanin Miliyan 7, Jahar nada Jami’oi guda biyu mallakin gwamnatin tarayya, da kuma guda mallakin gwamnatin Jaha, da kuma guda mai zaman kanta, wanda a yanzun gwamnatin Jigawan ta saya.

Dadi da kari, akwai sauran manyan makarantun Polytechnics da College of Educations, mallakar gwamnatin tarayya da Jahar Jigawa guda shida.

Amma fa duk da haka, Jahar na cikin jahohin da suke fama da kalubalen ilimin gaba da Sakandare (Educational Disadvantage States).

Bincike da yawa ya nuna cewa, dewa daga matasan Jahar Jigawa, mussaman ma mata, basa iya samun shiga Jami’a, bisa dalilai kamar haka:

Yanayin tattalin arziki.

Akasarin guraben da ake warewa mutanen Jahar Jigawa a Jami’oin Gwamnatin Tarayya a cikin jahar da wajen jahar wato (Catchment Areas), ba a iya cikewa, saboda tsadar kudin makarantar da a ke biya a wannan makarantu, da kuma yanayin talauci da wadatar mutanen jahar.

Jami’ar da tafi kowacce sauki ta Sule Lamido, mallakar Jahar Jigawa, ba zata iya bawa dukkanin masu neman gurbin karatun ba, saboda kullum karuwar yawan masu son cigaba da karatun a ke samu.

Yanayin al’adun mu da addinin mu.

Musamman ma yara mata, yanayin al’adun mu da mabanbantun karantarwar addinin mu, yayi tasiri, wajen shinge mata yan Jigawa zuwa makarantun gaba da sakandare dake nesa ko wajen jahar Jigawa.

Wannan ya sanya cinkoso don neman shiga Jami’ar Sule Lamidon.

Sayen Jami’ar Khadija.

Dalilai na cike gibin matasan Jihar Jigawa, musamman ma mata masu son zuwa jami’a, mallakar wannan Jami’ar ta Khadija zai taimaka wajen cike wannan gibi kwarai da gaske.

In har za a iya tafikar da wannan Jami’ar kamar yadda ake yi a Sule Lamido, Jahar Jigawan kan iya samun gagarumin cigaba a harkar ilimi, musamman ma na Jami’a, ga yaya mata da sauran matasan mu.

Sayen wannan Jami’ar da wannan makudan kudin, kusan sauki ne ga jahar, domin a yanzu, takeoff na Jami’a ta soma karatu, ya wuce wannan kudaden.

Ganin wannan Jami’ar ta kafu, tana da institutional da programme accreditations.

Wannan kuma kan iya dacewa da manufofin wannan gwamnatin na habaka ilimi.

alhajilallah@gmail.com

About the author

admin

Add Comment

Click here to post a comment